Monday 9 June 2008

HIRA DA HAFSATU ABDULWAHEED

Gwagwarmayar jikanyar Mujaddadi a fagen rubutu

HIRA DA HAFSATU ABDULWAHEED

Macen da ta fara rubuta littafin hikaya a Arewa, wato HAJIYA HAFSATU AHMAD ABDULWAHEED, ta samu karramawa ta musamman daga {ungiyar Marubuta ta Nijeriya. Shin yaya ta ji a ran ta? Kuma ina ta sa gaba yanzu?


Daga IBRAHIM SHEME

HAJIYA Hafsatu Ahmad Abdulwaheed ita ce mace ta farko da ta rubuta littafi aka wallafa shi a Arewacin Nijeriya kwata. Littafin ta na farko, So Aljannar Duniya, ya fito cikin a 1972 lokacin da aka yi gasar marubutan Hausa, har ta zo ta biyu. Marubuciyar ta rubuta littattafai da dama wad'anda ba su fito ba, kuma ta dad'e ta na fad'i-tashin ganin yadda littattafan ta za su fito, amma rashin kud'i ya hana.

Kwanan nan, abubuwa biyu sun faru ga Hajiyar. Na farko, ana nan ana shirin fito da wasu daga cikin littattafan ta, ciki har da wani na gajerun k'irk'irarrun labarai. Na biyu, lokacin da aka yi wani gagarumin bikin karrama marubutan Arewa a Minna, Jihar neja, Hajiya Hafsatu ta na daga cikin marubutan Hausa da aka karrama da kyautar lambar girma.

Ba wannan ba ne karo na farko da na yi hira da Hajiyar, domin idan kun tuna a ‘yan shekarun baya mun tab'a kawo muku wata hira da ita. A wannan karon, mun tattauna ne kan wad'annan abubuwa biyu da su ka faru gare ta, wad'anda duk na alheri ne.

Wani abu da ya kamata ku sani shi ne, Hajiya Hafsatu ta na daga cikin manyan mutanen k'asar nan. Na farko, ita jinin Mujaddadi Shehu Usmanu D'anfodiyo ce. A Jihar Zamfara kuma, fitacciyar ‘yar siyasa ce, domin a zab'en 2003 da aka yi, ta yi takarar zama Gwamnar jihar. Ta na da ‘ya’ya maza da mata; d'aya daga cikin ‘ya’yan ta, Hajiya K'adiria Ahmad, ta tab'a aiki a gidan rediyon BBC a London, yanzu kuma babbar ma’aikaciya ce a wani kamfanin kula da filayen jiragen sama a Legas. Haka kuma wata d'iyar ta Hajiya Hafsatu, wato Hajiya Asiya, ta na auren tsohon Ministan Abuja, Malam Nasir El-Rufa’i. Hasali ma dai, mun yi wannan tattaunawar ne da ita a gidan shi Malam Nasir da ke unguwar Jabi, a Abuja, kwana d'aya bayan an karrama ta. To bugu da k'ari kuma Hajiya Hafsatu ta kafa tarihin kasancewa mace ta farko da ta wallafa littafin hikaya a Arewa.

Ran ki ya dad'e, ki na daga cikin marubuta na Arewa wad'anda aka karrama su da lambar girma a Minna. Yaya ki ka ji a kan wannan karramawa da aka yi maki?
Alhamdu lillahi, na ji dad'i sosai. Sai dai bak'in ciki na kawai shi ne, uba na da uwa ta da miji na ba su da rai, balle su san abin da na samu. Amma murna kam na yi murna k'warai da gaske. Alhamdu lillahi.

Wannan shi ne karo na farko da aka tab'a karrama ki a kan harkar rubutu?
E, an tab'a yi a Kano, har su ka ba ni kamar lambar girma haka. Amma gaskiya na manta lokacin. Ina jin bara ne ko bara waccan.

Su waye su ka yi waccan karramawar?
Wata k'ungiya ce ta matasa marubuta.

Yaya ki ke ganin batun karrama marubuta, wanda ba a cika yi ba, yanzu ga shi ana yi? A farkon shekerar nan an yi a Abuja, sai kuma ga shi an yi a Minna. Shin wannan ya fara sauya tunanin mutane ne game da marubuta?
Ina ganin ’yan Arewa sun fara gane muhimmancin marubutan su. Ka san a da mutanen mu ba su damu da marubuta ba, musamman ma dai mata, ba a cika gane muhimmancin mu sosai ba, saboda an d'auka rubuce-rubucen mu shirme ne; na soyayya kawai. To, ina ji yanzu lokaci ya zo da aka soma gane muhimmancin mu. Saboda haka aka k'irk'iro wannan. Ya yi daidai kuma ya kamata a ci gaba da yin haka d'in.

A wurin bikin wannan karramawar a Minna, lokacin da ake karanta tak'aitaccen tarihin ki, an nuna cewa ke jikanya ce ko jinin Mujaddadi Shehu Usman D'anfodiyo ce. Mutane za su so ki yi k'arin bayani a kan wannan salsala taki.
To, ni dai sunan uba na Alhaji Abubakar Garba, sunan baban sa Sa’idu. Sa’idu kuma Hayatu ne ya haife shi. Hayatu kuma Sa’idu ne ya haife shi. To, shi kuma Sa’idu Muhamman Bello ne ya haife shi. Muhamman Bello kuma d'an Shehu Usmanu D'anfodiyo ne. Saboda haka ya zamana ni jikanyar jikanyar Shehu ce.

To, ko daga nan za ki ba mu tak'aitaccen tarihin ki?
An haife ni a 1952 a Kano, cikin unguwar K'ofar Mata, kuma na yi karatu a Shahuci da Provincial Girls School da Shekara Secondry School. Bayan nan na yi aure, inda miji na da shi ne manajan John Holt a Kano, daga baya aka mayar da shi Gusau. Bayan nan na yi ‘enrolling’ a Beneth Correspondence College, Landan, inda na d'an k'ok'arta na sami difloma. To, bayan nan dai na ci gaba da rubuce-rubuce. Na yi d'an aiki tak'aitacce a Kano, kamar part-time haka a gidan Rediyon Kano, amma ban dad'e ba, saboda ban dad'e da somawa ba na koma Gusau d'in. To, bayan nan dai sai rubuce-rubuce kawai da na ci gaba da yi a gida.

A bincike da na yi na fahimci cewa ke ce mace ta farko a Arewa da ta fara wallafa littafin k'irk'ira, wato littafin ki So Aljannar Duniya. Shin ki na da masaniyar cewa mata sun yi rubutu kafin ke ko kuwa a iyakar sanin ki ke ce ki ka fara d'in?
To, gaskiya ni dai ban tab'a ganin littafin wata ba ko da a jarida ko a wani guri da aka ce ta yi rubutu, sai da nawa ya fito tukunna. To, kuma bayan nawa ya fito - ina ji da kusan shekara 12 ma - na Zaynab Alk'ali ya fito. Koda ya ke akwai bambanci tsakanin nawa da ita, don ita na Turanci ta yi, ni kuwa da Hausa na yi.

Ko za ki gaya mana tarihin rubuta So Aljannar Duniya? Na farko ma dai menene ya fara ba ki tunanin rubuta littafi a lokacin da mata ba sa yi?
To, gaskiya a makarantar da na yi an d'an ba mu k'arfin gwiwar rubuta ’yan labarai a aji, har mu kan karb'i ’yan kyautuka a kai. A lokacin da na rubuta wannan ma da Turanci na soma rubuta shi duk da cewa Turancin nawa bai nuna ba, saboda yaya ta da ta auri Balaraben Libya ta sami ’yan tangard'od'i wajen dangi, haka da iyaye, wad'anda ba su so ta auri wani bak'o ba. To, daga baya kuma bayan na rubuta wannan sai na zo na auri wani Balaraben Yemen. To, sai labarin ya zamo kusan iri d'aya ne. To, da na rubuta shi da Turanci ban sami bugawa ba har lokacin da kamfanin NNPC Zaria ta yi gasa d'in nan, sai na fassara shi da Hausa na shiga gasar. A 1970 kenan. Na sami zuwa ta biyu a matsayi na na mace kad'ai da ta shiga wannan takara. To, bayan nan ne aka buga shi a 1972.

Tunda da Turanci ki ka fara rubuta shi, da yaya sunan sa?
Wallahi a lokacin ban sanya ma sa suna ba, don d'aya daga cikin abin da su ka hana ita yayar tawa a buga littafin shi ne mu na ta k'ok'arin mu ga wanne irin suna ya kamata a sanya masa. Saboda haka a lokacin ban sanya masa suna ba. (Murmushi) Amma dai Malam Sheme ya sanya masa suna a jarida (Weekly Trust); na gani. To, ina jin idan za mu yi shi da Turanci abin da za mu kira shi kenan.

Akwai yiwuwar za a fassara shi ne nan gaba?
E. An ma fassara shi da Turanci da Filatanci, kuma Jami’ar Usmanu D'anfodiyo, Sokoto, sun yi shi da Arabiyya. To, amma dai duk da haka har yanzu babu wanda aka rubuta a ciki.

Me ya tsayar da aikin bugun?
Gaskiya rashin kud'i ne a lokacin. Amma shi na Arabiyyar na sami wani mutumin Saudiyya da ya ce zai buga. To, amma abin bak'in ciki na yi gobara a 1995, saboda haka wannan kwafin na Arabiyya d'in ya k'one, kuma na yi k'ok'arin samun kwafi a hannun jami’ar ta Sokoto, don in kwafa, ban samu ba. Amma yanzu wani yaro ya sake buga shi da Larabci d'in. Saboda haka yanzu ina da rubutun hannu na Larabci d'in.

Labarin So Aljannar Duniya labari ne na Fulani, ku kuma ga shi a gari ku ke zaune. Me ya ba ki tunanin ki rubuta labarin Fulani maimakon labarin Hausawa wanda ki ka fi sabawa da shi?
To, ai ni Bafillatana ce, kuma duk da yake mu na cikin Hausawa, gidan mu ba mu zubar da yawancin al’adun mu na Fulani ba, domin ba a ma Hausa a gidan mu. Idan yaro ya tashi ba ya yin Hausa sai ya kai irin shekara bakwai d'in nan; sannan ya soma fita waje, ya koyi Hausa. Saboda haka ba wai wani abin a zo a gani ba ne don na rubuta al’adun mu.

Bayan wannan littafi sai aka d'auki tsawon lokaci ba ki yi wani littafin ba har zuwa lokacin da ki ka yi ’Yar Dubu Mai Tambotsai. Me ya sa aka sami wannan tsawon lokaci, kuma shekara nawa aka yi a wannan tsakanin?
Gaskiya ban san yawan shekarun ba, amma ina da littattafan da ma a rubuce; bugawa ne kawai ba a yi ba, saboda yanayin yadda babu kud'in da mutum zai buga d'in.

Wani abu da mu ka yi la’akari da shi shi ne, a matsayin ki na wacce ta soma rubuta littafin k'irk'ira a Arewa, sai ya kasance k'waya biyu kad'ai ki ka rubuta, ban da littattafan addini da mu ka san kin rubuta daga baya. Me ya sa ba ki rubuta littattafai da yawa ba kamar yadda sauran marubuta su kan yi?
(Murmushi) A’a! don littattafai ina da littattafai da dama; matsalar dai yadda na gaya maka ita ce bugawa. Domin ni ina ganin in buga su da k'ark'o sosai, wato abin da Bature ya ke cewa da quality, ya fi in buga su irin yadda sauran mutanen mu su ke yi da araha d'in nan su shiga kasuwa. To, shi ne kawai matsalar da ta hana ni bugawa da yawa, su fito. Amma akwai su nan a ajiye.

Ki na ta kukan rashin kud'i, amma wasu za su kalle ki a matsayin attajira, saboda ’ya’yan ki manya ne; an san su na auren manyan mutane da sauran su, kuma ke d'in ma dai babba ce. Anya za a yarda da maganar rashin kud'in nan, na dai a buga littafi?
A’a, to ai kamar nawa da na ke yi su na da tsada da yawa. Ka ga kamar wanda za a fitar wannan watan - Saba D'an Sababi - na k'irk'irarrun k'ananan labarai, abin da na biya mai bugawar shi ne N200,000 a kan kwafi 1,000 kacal. To, ka ga kuwa kud'in ba kad'an ba ne kenan. Kuma yara su na yin iyakar gwargwadon iyawar su, amma kowa ya na da iyali na kan su; ba za ka d'auki nauyin da ya fi k'arfin mutum ka d'ora masa ba, ballantana tun da baban su ya rasu. Kuma duk ba su dad'e da kawo k'arfi ba ai, saboda ba su dad'e da gama makaranta da kama aiki ba. To, ka ga akwai matsaloli da yawa a irin wannan.

Sannan kuma kallon kud'i da ake yi min, to alhamdu lillahi, sai in ce Allah ya k'ara min! Amma dai suna ne. Sarakuta kuma da masu kud'i, wannan ba hujja ba ce ta mutum ya na da shi. Domin sai surukin ya bayar sannan za ka karb'a. To, saboda haka ana dai k'ok'artawa. Yanzu dai mun yi da su za a tara duk ’yan rubuce-rubucen a tsinci wanda za a tsinta, su had'a kud'i su buga, wanda su ka ga ya dace da wanda za su iya.

Yanzu kin nuna mana cewa a a aiki a kan sabon littafin ki. Shi ma na k'irk'ira ne kenan?
E, na k'irk'ira ne. Wato na rubuta k'ananan labarai guda 46, wad'anda mu ka ce za mu kasa su kamar kashi uku ko hud'u. Ya danganta da dai yadda abin ya ke. To, kashi na farko ne zai fito; ya kamata ma a ce tun bara ya fito. To, harkar masu bugawa d'in ce…, sai dai ya yi min alk'awari, ya ce k'arshen watan nan idan Allah ya yarda zai fito. To, akwai kuma da yawa littattafan ai. Akwai biyu ma da Hukumar A Daidaita Sahu ta Jihar Kano su ka d'auka za su buga, wanda na yi a kan mu’ujizojin Alk'ur’ani mai girma. Sannan akwai d'aya da na yi kan wani labari na gaskiya da na k'irk'iro na rubuta, na sanya masa suna Aibin Doka. To, sun d'auki wad'annan biyun za su buga.

Akwai yiwuwar ki rubuta wak'ok'i ko wasan kwaikwayo?
E to, biyu daga cikin k'ananan labaran nawa na mayar da su wasan kwaikwayo, sannan kuma ina da rubutattun wak'ok'i - amma na Turanci - da yawa, domin gaskiya na gwada rubutawa da Hausar, na kasa!

Ashe ki kan yi rubutu da Turanci? Amma har yanzu ba a ga ko guda d'aya ba!
Wallahi ina yi, amma duk dai harkar idan aka juya ta batun dai bugawa d'in ce. Har yanzu ban sami wanda zai d'auki nauyin bugawar ba. Ni kud'in ba su dame ni ba, amma dai a ce aikin ya fito, shi ne muhimmanci a wuri na, amma har yanzu ban sami wanda zai d'auki nauyin ba. Amma na Turancin dai a kwanan nan mu ka zauna da yara mu ka tsinci wad'anda za a buga d'in. To, ban san dai abin da su ke ciki ba dai yanzu, amma sun yi min alk'awarin za su buga, to amma ban san lokacin ba.

Me ya sa kamfanin Gaskiya Corporation ko NNPC Zaria ba su buga littattafan ki da yawa ba, musamman tunda a wancan lokacin su na cikin aikin buga littattafai da yawa, ba kamar yadda daga baya su ka durk'ushe ba?
Wallahi ni dai abin da su ka gaya min shi ne ba su da kud'i. Duk dai magana guda ce a lokacin da na kai musu nawa guda biyu, wad'anda har da ma na ‘Dare Dubu Da D'aya’ da na rubuta yadda yara za su iya karantawa, saboda na farkon nan bai kamata yara k'ananan su karanta shi ba. To, na rubuta daga na 1 zuwa na 5 kamar yadda aka yi shi na Hausa d'in nan. Har yanzu ma kwafin ya na hannun su, ba su dawo min da shi ba, don sun ce min yanzu su na ‘yan shirye-shiryen soma buge-bugen littattafai.

Yaya ki ke ganin harkar wallafa a Arewa?
To, gaskiya abin ya na da ciwo. Kuma duk a wasu taruka da aka yi na marubuta na kan bayar da shawarar cewa su kan su marubutan su na da laifi, saboda za a iya had'in gwiwa, a saka ‘yan kud'ad'e; kowa ya bayar da gudunmuwar sa, a had'a kud'in nan a ajiye. Idan marubuci ya rubuta littafi a duba, idan ya cancanta a buga shi, sai a d'auki nauyin bugawar. In ya so bayan an buga, an sayar ko an k'addamar, abin da aka sayar, sai a mayar a ajiye. Kuma nan gaba sai a sake samun wani ya yi. Amma duk shawarwarori na da na ke bayarwa, har yanzu babu wacce ta sami shiga.

Ita gwamnati da masu hannu da shuni fa?
To, gwamnati dai ba ta san da zaman marubuta ba, sai dai kwanan nan da ake ta abubuwan nan na ga gwamnatin Neja ta d'auki nauyi. To, kuma gwamnatin mu ma ta Jihar Zamfara ta yi alk'awarin za ta bud'e mana wani asusu wanda idan an yi littafi, a bincika shi a gani; idan ya cancanta, a buga. Sai mu yi fatan sauran gwamnoni za su yi koyi da su.

Wane kira za ki yi ga marubuta wad'anda ke kasa fito da littattafan su, har ma wani sai ya yi fushi ya daina?
Bai kamata mutum ya yi fushi ya daina ba, domin idan Allah ya ba ka basira, ka daina amfani da ita, kamar ka yi masa butulci ne. Shi kuma rubutu ko da mutum ba shi da rai ya na da amfani. Kamar yadda mu ka ga littattafan Shehu da Asma’u d'aruruwan shekaru ga su nan yanzu ana morar su. Saboda haka kada mutum ya bari. Kada rashin bugawar nan ta karya masa gwiwa; ya yi ta rubutun ya na ajiyewa har Allah ya kawo wanda zai zo ya buga masa. Saboda komai ya na da lokaci. Idan lokacin abu bai yi ba, babu yadda za a yi ka tilasta lokacin ya yi.

To, Hajiya mun gode, k'warai.
To, madalla. Ni ma na gode.

(An ciro daga mujallar Fim ta watan Yuni 2008)